Malamin makarantar Destiny Academy dake lalata da yara a babban birnin tarayya, Igoche Daniel Adah ya tsere daga gidan kurkuku na Kuje.
Malamin yana daya daga cikin mutanen da suka tsere a gidan kurkukun bayan ‘yan ta’addan ISWAP sun kai mummunan hari gidan.
Igoche Daniel Adah ya tsere ne bayan kotu ta daga shari’arsa zuwa watan Oktoba kafin ta yanke masa hukunci daidai da laifin daya aikata.
Kuma malamin yaki amincewa ya amsa kaifin da ake zargin shi da aikatawa.