Gwamnatin tarayya ta dorawa lemun kwalba da suka hada da kamfanonin Coke da Sprite sabon harajin Naira 10 akan kowace lita.
Ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a ganawa da manema labarai a ranar Laraba a Abuja.
Zainab tace shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da wannan mataki a sabuwar dokar kasafin kudin da ya sakawa hannu.
Zainab tace an kuma saka irin wannan haraji akan bangaren lafiya dana sikari. Tace harajin kan lemukan kwalban dan a rage yawan sugan da ake sha ne dake kaiwa ga cutar suga.