fbpx
Monday, January 18
Shadow

Likitoci 20 sun kamu da cutar Corona a jihar Kwara

Shugaban Kwararrun Likitoci na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH), Dokta Badmus Habeeb, ya bayyana cewa likitoci 20 sun kamu da mummunar cutar korona  a cikin makonni uku da suka gabata a jihar Kwara.

Da yake magana yayin ganawa da gidan talabijin na Channels Tv, Habeeb ya ce kungiyar tana yaki ne da cutar “bisa la’akari da wadatar kayan aiki”.
Ya lura cewa gano magungunan rigakafi ya kawo fata da kwanciyar hankali ga kowa.
A cewarsa, alluran riga-kafi sun tabbatar da cewa suna da inganci, ya kara da cewa ‘yan Najeriya suna bukatar yin allurar riga-kafi da zarar ta zo yayin da suke bin ka’idoji na COVID-19.
“Dole ne in sake nanata cewa wannan ba shi ne mafi kyawun lokuta ba a gare mu, da iyalanmu da majinyatan da abin ya shafa.
“Don haka, da alama ba za mu iya samun allurar nan da nan ba. Ya kamata jama’a su bi ka’idojin da aka shimfida kan rigakafin da kara yaduwar wannan kwayar cutar, “inji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *