Wednesday, June 3
Shadow

Likitocin jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki duk da gargadin gwamna El-Rufai

Kungiyar Likitocin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 2 saboda gwamnati ta yi watsi da bukatunta.

Jihar Kaduna tuni ta yi watsi da yajin aikin inda tace zata bude rijista dan ma’aikatan da zasu iya yin aiki da ita su saka sunayensu.

 

Saidai duk da haka likitocin sun yi zama inda suka sakawa wata sanarwa hannu wadda suka amince da tafiya yajin aikin.

 

A zaman da likitocin suka yi sun sun lura cewa jihar Kaduna ta zaftare musu kashi 25 cikin 100 na Albashinsu wanda kuma hakan baya cikin doka.

 

Sun bayyana cewa wannan abu yasa suna ganin ba’a damu dasu ba kuma gwamnati bata gode musu bisa aikin da suke yi dan haka an kashe musu kwarin gwiwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *