fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Limaman jihar Kaduna sun cimma matsayar cewa ba zasu yi sallar Idi ba

Kungiyar Limamin addinin Musulunci na jihar Kaduna sun cimma matsayar cewa ba zasu yi Sallar Idi ta karamar Sallah ba da ake tsammanin yi Ranar Asabar me zuwa.

 

Kungiyar ta bayhana cewa ta yi zama da gwamna malam Nasir Ahmad El-Rufai inda ta sanar dashi matsayinta.

 

Da yake magana a madadin limaman, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, idan aka bari ayi sallar Idin to za’a mayar da hannun agogo bayane kan nasarorin da aka samu a jihar na yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Ya bayyana cewa mutane a Najeriya ba kamar a kasar Saudiyya bane yanda za’a iya kayyade yawan wanda zasu fito sallah,yace idan akace misali mutum 50 su fita, mutane da yawa zasu fitone ta yanda ba za’a iya sarrafasu ba. Yace kuskuren kwana daya zai iya sawa a lalata nasarar da aka kwashe lokaci kamin a sameta.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

 

Malam ya kara da cewa, idan aka duba jihohi Irinsu Kano Jigawa da Yobe an samu mace-macen mutane da yawa amma a Kaduna ba’a samu wannan ba.

 

Dan haka yace kowa yayi sallarsa a gida.

 

Jihar Kaduna dai nada mutane 145 da suka kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.