Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Liverpool zata bar tauraron dan wasanta na gaba Mohammed Salah ya sauya sheka a wannan kakar.
Kungiyar ta dade tana kokarin shawo kan dan wasan ya sabunta kwantirakinsa amma abin ya citara, kuma gashi watanni 12 ne suka rage a kwantirakinsa.
Sannan kuma ana sa ran zata sayar dashi a yuro miliyan 60 idan har ta samu kungiyar da zata saye shi, don idan ba haka ba to zata rasa shi a kaka mai zuwa don zai tafi kyauta.
Idan Salah ya bar Liverpool a wannan kakar to tabbas kungiyar zatayi babban rashi don dama ta riga ta rasa tauraron san wasanta Sadio Mane, wanda ya koma Bayern Munich.