fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

“Lokaci na kara kurewa fa”>>Farfesa Shuaibu ya gargadi gwamnatin tarayya kan ceto mutanen da akayi garkuwa dasu a jirgin kasa na Kaduna

Farfesa Shuaibu Mustapha, malami a makarantar jami’ar Ado Bayero ta jihar Kano yayi kira ga shugaba Buhari cewa ya gaggauta ceto mutanen da akayi garkuwa dasu a jirgin kasa na Kaduna.

Ya bayyana hakan ne yayin daya ke ganawa da manema labarai na DailyPost inda ya bayyana masu cewa lokaci na kara kurewa.

Kuma yace yanzu kimanin kwanaki 90 kenan mutanen suna hannun ‘yan bindigar gashi ba wata cikakkiyar kukawa suke samu ba, saboda haka ya kamata gwamnatin tarayya tayi wani abu akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.