Yayin da zaben shekarar 2023 ke gabatowa, manyan ‘yan takatarar dake neman kujerar shugaban kasar Najeriya na cigaba da yakin neman zabe domin samun nasarar maye gurbin Buhari a Villa.
Yayin da shi kuma dan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu har yanzu yake cigaba da fafutukar neman tsayayyen abokin takararsa.
Inda shi kuma dan takarar Labour Part Peter Obi yake cigaba da samun karbuwa kuma da yiyuwar zai bada mamaki duk da cewa hasashe ya nuna cewa ba zaiyi nasara ba.
Sai Alhaji Atiku Abubakar dan takarar PDP wanda shima a tsaye yake don ganjn cewa yayi nasarar lashe wannan zaben domin ya maye gurbin Buhari a Villa, saboda ya dade yana burin hakan.