A wata hira da yayi da me jaridar Sun tun shekarar 2012, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi batutuwa da dama wadanda suka ja hankulan mutane sosai, jaridarce dai ta wallafa wannan labari daga jiya zuwa shekaranjiya, daya daga cikin batutuwan da sukafi daukar hankulan mutane a hirar da shugaba Buhari yayi da me jatidar shine cewa da yayi lokacin yana matashi yayi ‘yan mata kuma yasha taba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Me hira dashi dinne ya tsokano labarin inda ya tambayeshi wai yaji ance shugaba Buharin ya taba shan taba a shekarun baya, sai ya amsa mishi da cewa, tabbas yasha taba a baya amma a shekarun 1977 ya daina shan tabar kamin ya zama shugaban kasa.
Shugaba Buharin ya kara da cewa amma giyace bai taba dandanawaba saboda addininshi ya hana hadui kuma da cewa akwai yiyuwar idan mutum yasha giya gwalba daya zaiji yana so ya kara shan wata kwalbar, hakan zaisa mutum har ya shiga tambele yayi abinda be kamataba, yace yana so ya kasance koda yaushe yana cikin shirin kota kwana.
Da me tambayar ya tambayi shugaba Buhari akan ‘yan mata kuwa, shugaban ya kara da cewa Eh yayi ‘yan mata, an kara tambayarshi guda nawa yayi?, sai yayi dariya yace ina fatan ba zaka wallafa wannan bangaren ba saboda matata zata karanta.
Wani batu shima da ya kara daukar hankulan mutane dangane da wannan hira shine inda me tambayar ya tambayi shugaba Buhari cewa duk ga abokanshinan da suka rike mukaman shugaban kasa amma sunyi kudi shi kuma gashi kamar bashi da irin kazaman kudinnan, sai yace, shidai bai san yanda ake neman kudi sosai ba.
Domin karanta cikakkiyar wannan hira cikin harshen turanci sai a danna nan
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});