fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Luiz Suarez ya haskaka sosai bayan yaci kwallaye biyu a wasan shi na farko a kungiyar Atletico Madrid

Kocin Atletico Madrid Diego Simone ya saka sunan sabon dan wasan shi wato Luiz Suarez cikin yan wasan da zai yiwa canji a  wasan su da Granada yau, kuma tsohon dan wasan Barcelona ya kalli yadda Diego Costa da Andrea Correa da kuma Joao Felix suka sa Madrid take jagorantar wasan da kwallaye uku cikin mintina 65 daga benci.

Simone ya sako Suarez wasan ana sauran mintina 20 a tashi kuma kokarin daya yi ya nuna cewa Barcelona ta aikata babban kuskure data bar tauraran dan wasan ta ya koma kungiyar hamayyar ta a gasar La Liga. Mintina biyu kacal Suarez ya dauka kafin ya fara nuna bajintarsa a Madrid  yayin daya taimakawa Lucas Llorente ya zira kwallo guda sannan kuma shima bayan mintina 13 ya zira kwallon shi ta farko a kungiyar.
Luiz Suarez ya kara zira kwallo guda bayan mintina takwas wadda tasa aka tashi wasan 6-1, kuma dan wasan Uruguay din ya zamo dan wasa na farko daya ci kwallaye biyu kuma ya taimaka akaci kwallo a wasan shi na fako a kungiyar Atletico Madrid.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.