Saturday, March 28
Shadow

Ma’aikacin FIRS ya bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Wani Ma’aikacin hukumar dake kula da karbar Haraji ta kasa, FIRS me suna Salihu Umar ya bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter inda yace ya sanar da jami’an lafiya.

 

A lokacin da yake rubuta sakon yace suna kan hanyar zuwa gida su tafi dashi.

 

 

A baya dai hukumar ta FIRS ta karyata cewa babu ma’aikacinta ko daya dake dauke da cutar.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *