fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Ma’aikatan Lafiya Na Jihar Bauchi Sun Janye Yajin Aiki

Kungiyar hadin gwiwar Ma’aikatan Lafiya da Majalisar kwararru kan Kiwon Lafiya, reshen jihar Bauchi, sun dakatar da yajin aikin na sai baba ta gani wanda ya fara a ranar 6 ga watan Agusta.

 

Sakataren kungiyar ta JOHESU a jihar, Usman Danturaki, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Bauchi, ya ce “ba za a sami kwanciyar hankali ba muddin gwamnatin jihar ta ci gaba da taba albashin su”.
Ya ce, duk da haka, ya ce ana ci gaba da tattaunawa don magance matsalolin gaba daya.
Danturaki ya ce kungiyar ta ayyana yajin aiki ne domin nuna rashin amincewa da zaftarewar kudaden da gwamnatin jihar ta yi daga albashin watan Yuni da Yuli na shekarar 2020.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *