fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Ma’aikatan majalisa a Najeriya sun janye yajin aiki

Kungiyar ma’aikatan majalisar tarayya a Najeriya ta janye yajin aikin da ta shiga.

Ma’aikatan sun shiga yajin aikin sai yadda hali ya yi a ranar Litinin ta makon da ya gabata, don matsa lamba na a biya su kudin alawus da suke bi.

Jaridun cikin gida sun ambato Shugaban na PASAN Sunday Sabiyi yana cewa sun aminta da janye yajin aikin ne bayan cimma wata matsaya da Shugabannin majalisar.

Sai dai PASAN ta yi barazanar sake tsunduma wani yajin aikin, matsawar Shugabancin majalisar ya gaza aiwatar da abinda suka cimma daga nan zuwa karshen Yuli.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *