fbpx
Tuesday, August 4
Shadow

Ma’aikatar Kudaden Shiga Ta Jihar Kano Ta Kori Ma’aikata 368

Hukumar kula da kudaden shiga ta jihar Kano ta kori ma’aikata 368, wadanda suka hada da ma’aikata 308 da kuma masu ba da shawara 60.

 

Lokacin da aka nemi tabbatar da abin da ya yi a ranar Laraba, Shugaban zartarwa na KIRS, Alhaji Bala Inuwa, ya danganta lamarin da mawuyacin hali na ayyukan, sakamakon barkewar annobar cutar korona, wanda ya gurgunta ayyukan kasuwanci da tattalin arziki a kasar.
A cewarsa, kafin zuwan cutar korona, hukumar KSIRS na samun sama da kusan Naira biliyan biyu a kowane wata, yana mai nadamar cewa zuwa yau, abin da ya tabarbare ya kai ga karancin samun tsakanin naira miliyan 500 zuwa 700 miliyan kowane wata.
A irin wannan yanayin, ya bayar da hujjar cewa shawarar da ta dace hukumar ta dauka, don ta ci gaba da gudana, ita ce sauke nauyi, tare da kara cewa wannan ci gaba, ya samar da shawarar da aka gudanar na rage ma’aikata na dan lokaci.
Inuwa, ya kuma yi alkawarin cewa, za a sake dawo da ma’aikatan na wucin gadi 308, da zaran an samu farfadowar kudin hukumar ta KIRS.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *