fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Mabiya Shi’a Sun Gudanar Da Zanga-zangar Lumana

A yau Alhamis 28/4/2022 Ƴan shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun fara zanga-zanga da suka saba duk Juma’ar karshe na watan Ramadan. Sun fara zanga-zangar ne tun yau Alhamis a garin Kaduna. Inda suka fito mazansu da matan su manya da yara, suna tafiya suna faɗin Free Palastinu, hannayen su dauke da tutoci kalas tutar Palastine.

Wannan zanga-zangar lumanar dai sun saba yin ta ne duk shekara domin nuna goyon bayan su ga al’ummar Falasɗinawa da Isra’ila ke musu kisa ba dare ba rana tsawon shekaru, ƴan shi’ar dai suna kiran wannan zanga-zangar ne da Muzahharar Qudus.

Karanta wannan  Peter Obi ya fice daga jam'iyyar PDP

Daga Muhammad Sadis

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.