Emmauel Macron ya sake yin nasarar lashe zaben shugabancin kasar Faransa inda ya doke marine Le Pen.
Kungiyar masu zefa kuri’u ta bayyana cewa Macron nada kashi 57 zuwa 58 na zaben, yayin da shi kuma Le Pen keda kashi 42.
Bayan an tabbatar da Macron a matsayin shugaban kasar, ya mika sakon godiyarsa ga mabiyansa inda ya sha alwashin magance matsalolin da kasar ke fama dashi.