Thursday, July 18
Shadow

Mafarauci ya harbe abokin farautarsa inda yayi tsammanin dabbace

An kashe wani mafarauci Sunday Ijiola a Yewa jihar Ogun inda aka yi tsammanin dabbace.

Atanda Agbobiado ne yayi kisan ranar 28 ga watan Mayu.

Mafarauta kusan 15 ne suka fita farautar inda suka raba kawunansu a cikin daji.

Da Atanda ya tabbatar da abinda ya aikata sai ya tsere.

Wanda aka harba din dan kimanin shekaru 43 ya mutu akan hanyar zuwa Asibiti.

Kakakin ‘yansandan jihar Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna bincike akai.

Karanta Wannan  NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na naira biliyan 2.1 a Legas da Fatakwal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *