fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Mafi Munin Aiki a Najeriya shine ka zama Gwamna, Kowa kallon barawo yake ma>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ‘yan Najeriya da dama nawa gwamnoni mummunan Kallon cewa barayine kawai.

 

Gwamnan ya bayyana hakane a ganawar da yayi da gidan talabijij din Channelstv inda yace mutane na tunain gwamnoni basa komai in banda satar kudi, wasu na tunanin ana baiwa gwamnoni kudin tsaro wanda suke yanda suka ga dama dasu.

Yace amma maganar gaskiya itace aikin gwamna shine aiki mafi muni a Najeriya, yace Gwamnatin tarayya na iya buga kudi amma su basa iya bugawa sannan akwai iyakar da aka kayyade musu akan ciwo bashi.

Karanta wannan  Sakamakon jarabawata ta WAEC ta bata amma tayi matukar kyau don ni ne dalibi na biyu dayafi kokari a shekarar, cewar mataimakin Atiku, Okowa

 

Yace aikin gwamna na daya daga cikin ayyuka mafiya wahala a Duniya, yace in banda Legas yawanci jihohin Najeriya da kudin da gwamnatin tarayya ke aika musu suke Dogara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.