fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Maganar maja tsakanin NNPP da Labour Party ta mutu murus tun tuni, cewar babban darektan Peter Obi

Babban darektan kungiyar dake yiwa Peter Obi yakin neman zabe, Doyin Okupe ya bayyana cewa maganar maja tsakanin NNPP da Labour Party ta mutu makonni hudu da suka gabata.

Inda yace Kwankwaso yana so yayi amfani da farin jinin Obi ne don yayi nasarar lashe zaben shekarar 2023.

Saboda haka su sun janye ra’ayi akan hakan tun tuni amma NNPP ne suke cigaba da matsa masu akan maganar domin suyi amfai da Obi.

Ya bayyana hakan ne yayin daya ke ganawa da Channels inda yace basu sanar da hakan a kafafen sada zumunta bane saboda sanin ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.