Thursday, July 18
Shadow

Maganin ciwon kai kowane iri

Ciwon kai na da magunguna na turawa wanda suke aiki da kyau, musamman idan ba me tsanani bane sosai.

Magungunan dake magance ciwon kai sun hada da.

Aspirin

Paracetamol

da Ibuprofen.

Hakanan masana sunce kwanciya a cikin daki me duhu, wanda babu hasken wutar lantarki ko na rana na taimakawa wajan magance matsalar ciwon kai.

Abincin da ake son me yawan ciwon kai ya rika ci:

Nama

Ganye, irin su Kabeji, Zogale da sauransu.

Gyada.

Madara.

Kwai.

Ana kuma amfani da wadannan dabarun na kasa dan magance matsalar ciwon kai:

Amfani da tsumma me sanyi a dora a goshi.

Ko Amfani da tsumma me dumi a dora a goshi ko a bayan kai.

Karanta Wannan  Maganin cizon sauro

Ana amfani da Ganyayyaki da aka saka a firjin suka yi sanyi.

Ana iya yin wanka da ruwan sanyi.

Hasken wutar lantarki, Hasken waya, ko na kwamfuta ka iya sa maka ciwon kai dan haka ana iya kashewa ko a rage hasken.

Cin cingam, Goruba da sauransu na iya kawo ciwon kai, idan kana jin ciwon kai, kada ka yi tauna sosai da bakinka, ko kuma ka cika bakinka da abinci kananci da kyar.

Kishirwa na sa ciwon kai, dan haka ka sha ruwa sosai dan samun warakai ciwon kai.

Shan ruwan citta na magance ciwon kai.

Kadan murza kanka, watau Massage, da wuyanka, hakan na kawo saukin ciwon kai.

Karanta Wannan  Abincin dake sa kiba, Karin kiba cikin sauri

Idan ciwon kai yayi tsanani, a Tuntubi Likita.

Wadannan bayanai duka mun samo sune daga kafofi wadanda likitoci suka amince dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *