Sunday, July 21
Shadow

Maganin ciwon zuciya na Gargajiya

Ciwon zuciya wanda yayi tsanani yana bukatar kulawar kwararren likita, saidai idan bai yi tsanani ba, ana iya amfani da magungunan gargajiya wajan maganceta

Irin ciwon zuciyar da ake magancewa a gida shine wanda baya faruwa a kullun, watau na dan lokacine, sai kuma damuwa, da daurewar gabobi, sai da yawan gyatsa.

Wasu lokutan akwai wahala wajan gane ko banbance kalar ciwon zuciyar da ya kamata a magance a gida da wanda ya kamata aje Asibiti.

Idan aka ji wadannan alamu na kasa to a je Asibiti:

Ciwin kirji idan ya yi tsanani yana daurewa, yayi nauyi ko yana nusar mutum.

Idan mutum ya ji kamar zuciyarsa zata buga.

Karanta Wannan  'Jami'an tsaro shida na cikin mutanen da aka kashe a harin Katsina'

Idan aka ji alamar numfashi na neman daukewa.

Idan ba’a ji wadannan alamu na sama ba to za’a iya gwada maganin gargajiya na gida kamar haka:

Ana iya samun tsumma me kyau a saka kankara a cikinsa a nade a rika dorawa akan kirji, ko kuma a sakashi a cikin firjin idan yayi sanyi a rika dorawa akan kirji.

Shan ruwan zafi ko Shayi. Amma abinda masana suka fi bayar da shawara shine a sha ruwa Zobo me dumi.

Tafarnuwa: Rahotanni da yawa sun ce tafarnuwa na maganin ciwon zuciya.

Ana iya hada ta da kanumfari. Sannan kuma ana iya hadawa da madara. Saidai maimakon a shata, zaifi amfani idan aka tauna tafarnuwar.

Karanta Wannan  Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Idan ciwon zuciyar ya motsa, ana son mutum ya kwanta ya dora kansa akan Fillow, hakan na taimakawa sosai.

Ana iya shan ruwan citta ko shayinta, shima masana sun yi amannar yana taimakawa sosai wajan magance matsalar zuciya.

Hodar kurkur ma ana hadawa da ruwan madara me dumi a sha. Ana sha ne kamin a kwanta bacci, yana taimakawa sosai wajan maganin ciwon zuciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *