Sunday, July 21
Shadow

Maganin istimna’i na gargajiya

Maganar gaskiya itace babu wani maganin istimna’i, duk wanda yace zai sayar maka da maganin Istimna’i to karya yake kudinka kawai zai ci.

Dalili kuwa shi Istimna’i dabi’a ce wadda sha’awa ke jawo ta, ita kuwa sha’awa, muddin dan adam yana da rai da lafiya kuma zai ci abinci, yana cikin kwanciyar hankali, sha’awa zata zo.

A likitance babu maganin istimna’i, saidai yawan yinshi alamace ta cewa mutum na cikin damuwa.

Wasu abubuwan da mutum zai iya amfani dasu wajan magance matsalar Istimna’i sun hada da yin Azumi, saboda yana rage sha’awa.

Mutum ya daina zama baya aikin komai, ka samu wani abu da zai rika dauke maka hankali, karka rika zama baka aikin komai.

Karanta Wannan  Nasiha akan rayuwa

Mutum ya dainaa warewa shi kadai, a rika shiga cikin mutane ana mu’amala.

A daina kallon Fina-finan batsa, yawan kallon Fina-finan batsa na taimakawa wajan aikata Istimna’i, dan haka a daina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *