Saturday, July 13
Shadow

Maganin pimples da black spot

Ana samun maganin pimple da black spot a gida ba tare da amfani da maganin asibiti ba.

Hanyoyin magance pimples da black spot sun hada da:

Amfani da Aloe Vera: Ana samun ruwa ko man Aloe Vera wanda ba’a hadashi da komai ba a shafa a fuska wanda yana maganin pimples da black spot sosai.

Idan ba’a samu na kemis ba, ana iya hadawa a gida ta hanyar yanko ganyen Aloe vera a fere koren bayan a tatso ruwan a rika shafawa a fuska.

A lura idan fuska ta nuna alamar reaction, sai a daina amfani dashi a tuntubi likita, idan kuma bata yi ba, sai a ci gaba har fuska ta dawo daidai. Ana iya karanta karin bayani kan amfanin Aloe vera wanda muka rubuta

Karanta Wannan  Gyaran fuska da man kwakwa

Ana kuma amfani da Man Zaitun wajan magance matsalar pimples da black spot:

Ana amfani da man zaitun kai tsaye a shafa a fuska ba tare da hadashi da komai ba. A rika shafawa akai-akai dan samun sakamako me kyau. Akwai karin bayani da muka yi akan amfanin man zaitun wajan gyaran fuska.

Ana amfani da Madara wajan kawar da kawar da black spot da Pimples.

Madara na daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajan kawar da pimples da black spot a fuska. A samu madara ko kyalle me kyau a yi amfani dashi wajan shafa madarar a fuska bayan an kwaba da ruwa. Akwai cikakken bayanin amfanin Madara wajan gyaran fuska da muka yi.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da zuma

Amfanin Zuma wajan cire black spot da Pimples:

Ana amfani da zuma wajan gyara fuska a kawar da black spot da pimples su fita gaba daya. Yanda ake yi shine, Ana samun zuma me kyau wadda ba hadi a shafa a fuska, ana iya kara mata ruwa dan rage dankonta. Idan ta dauki lokaci sai a wanke. A rika maimaitawa har a samu sakamko me kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *