Wednesday, July 24
Shadow

Maganin rage zafin nakuda

Radadin nakuda na daya daga cikin manyan abubuwan dake kayar da gaban mata wanda ke sa su rika neman abinda zai kawo musu saukinsa.

A wannan rubutu, zamu kawo muku magunguna na gargajiya wanda likitoci suka tabbatar suna aiki wajan rage zafin Nakuda.

Shan Zuma

Ta tabbata likitoci sun ce mace me ciki dake shan zuma na samun saukin Nakuda sosai ba kadan ba. Hakanan a lokacin nakudar ana iya baiwa mace me ciki zuma ta rika sha, shima yana taimakawa sosai wajen rage radadin Nakudar.

Amfani da Zuma da Dabino

Hakanan kuma Hada zuma da Dabino a yi blendinsu a sha, shima yana taimakawa rage zafin nakuda da sawa ta a samu nakuda wadda bata da tsawo, watau a haihu da wuri. Wannan sahihin maganin nakuda ne dan an kwada akan mata da yawa wanda aka yi bincike dasu kuma yayi aiki.

Karanta Wannan  Kumburin kafa ga mai ciki

Amfani da man kwakwa

Hakanan a yayin da ake kusa da haihuwa, masana sun ce a rika shafa man kwakwa a tsakanin gaban mace, watau farji da inda ake kashi, saboda budewar farji yayin haihuwa, hakan yana taimakawa wajan hana yagewar farji a yayin haihuwa.

Hakanan Ana shan man kwakwa a abinci idan aka kusa haihuwa wanda shima yana taimakawa kuma bashi da illa amma a tabbatar an samu me kyau wanda ba’a mai hadi ba.

Hakanan ana son wasu su kasance da macen da ta fara nakuda su rika bata kwarin gwiwa akan haihuwar, ana kuma iya mata tausa a gadon baya, kafafu da sauransu.

Zata iya yin wanka, ko ta rika dan zagayawa ko ta rike wani abu a hannu tana matsawa.

Karanta Wannan  Cikin wata hudu

Ana kuma cin wadanan ‘ya’yan itatuwa san rage radadin nakuda:

Ayaba.

Ruwan Kwakwa.

Kwai: Ana iya cin kwai kamin a tafi asibiti,idan haihuwar ta asibitice.

Kankana.

Ana shan Yegot, Yoghurt.

Cin Dabino: Wani bincike ya gano cewar,matan dake yawan cin dabino akai-akai suna samun saukin haihuwa sosai. Binciken ya bayar da shawarar cun dabino guda 6 kullun, wata daya kamin ranat Haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *