fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Magidanci da matarshi ta haifi ‘yan uku ya so tserewa amma an dawo dashi

Wani magidanci, Cissé Abdullahi dake Legas ya so tserewa bayan da matarsa ta haifi ‘yan uku a lokaci guda.

 

Yace a lokacin da matar tasa ta haihu N3,500 ne kawai a Aljihunsa, yace kuka ya ga baida mafita kawai shine ya tsere.

 

Dan shekaru 37 ya bayyana cewa, a Asibiti an gaya musu ‘yan Biyu ne matar tasa zata haifa amma yanzu sai ga ‘yan uku, shiyasa abin ya gigitashi.

 

Yace ya kama hanyar zuwa kasar Benin Republic, sai ya hadu da abokinsa wanda ya tambayeshi ina zashi.

 

Yace dole ya gayawa abokin nasa halin da yake ciki, koda abokin nasa ya ji haka, sai yace bai kamata ya tsere ba, kamata yayi ya koma gida kuma yayi alkawarin taimaka masa.

Karanta wannan  Yajin aikin ASUU ya kai kwanaki 140 ana yi

 

Da yake ci gaba da baiwa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN labarin yanda lamarin ya kasance, Abdullahi yace har zuwa yanzu taimakon da ya samu daga abokinsa ne kawai yake amfani dashi.

 

Yace yana neman gwamnatin jihar Legas ta tallafa masa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.