fbpx
Friday, August 12
Shadow

Magidanci dan shekara 35 ya yiwa marainiya fyade a jihar Delta

Hukumar ‘yan sanda ta damke wani magidanci dan shekara 35 dayake lalata da marainiya yar aji na biyu a makarantar sakandiri, watau SS2.

Yarinyar ta kasance diyar ‘yar uwanshi data mutu kuma ya dade yana aikata lalata da yarinyar a cewar likitan daya duba ta.

Inda yace yaji mata babban rauni a farjinta amma shi wanda ake tuhuma yace sau uki kacal ya taba yin lalata da ita.

Inda shi kuma likitan yace alamu sun nuna cewa ya dauki tsawon shekaru uku yana lalata da yarinyar. Abinda yasa yarinyar taki fada shine yace zai daina biya mata kudin makaranta kuma zai kashe ita idan ta bari wani ya sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published.