Jami’an tsaron ‘yansanda sun kama wani mutum da shekaru 49 me suna Lawrence Itape bisa kashe matarsa, Rebecca.
Maganar ruwan wankane ya hadasu wanta ta kai cece-kuce ya barke a tsakaninsu.
Magidancin ya bayyana cewa, ta rika zagin mahaifansa wanda dama ta saba hakan duk sanda rikicu ya barke tsakaninsu, dalilin hakane shi kuma ya shiga dakin girki ya dauko wuka ya caka mata a wuya wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Benjamin Hudenyin ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ana ci gaba da bincike.