fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

Magidanci ya kashe kansa a Kano ta hanyar Rataya

Wani magidanci ya rataye kansa da kansa a unguwar Sauna Kawaji da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

 

Magidancin Mai suna Sabi’u Alhassan mai shekaru 62, an samu gawarsa ne a gidansa bayan matarsa ta fita unguwa.

 

Shaidun gani da ido sun shaidawa hutudole cewa su ma ba su san dalilin da ya sa wannan dattijo ya aikata wannan aika aika ba.

 

Duk da ya ke cewa babu tabbacin shi ne ya kashe kansa, amma hukumar yan sanda na jihar Kano sun fara binciken musabbabin wannan abu mai rikitarwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *