Magidanci Taofeek Gbolagade ya lakadawa matarsa duka saboda bata hada masa kayan Sahur ba.
Lamarin ya farune a Ogbere jihar Oyo, kuma gashi matar tasa na da ciki.
Makwabta sun bayyana cewa dama ya saba dukan matar tasa kan abubuwan da basu taka kara suka karya ba.
A wannan karin ma dan bata hada masa kayan Sahur ba shine ya hauta da duka. Ta samu dai ta tsere gidan iyayenta.
Kakakin ‘yansandan jihar, Adewale Osifeso ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna kan bincike.