fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Magoya Bayan Malami Sun Nuna Takaicinsu da Janyewar Takarar sa

Daga Tukur Sani Kwasara

Magoya bayan Ministan Shari’a, Abubakar Malami sun nuna takaicinsu game da janyewar takararsa ta neman kujerar Gwamnan Jihar Kebbi.

Magoya bayan minstan dai sun nunar da cewa jikinsu ya yi sanyi ganin yadda aka dade ana fafatika wajen ganin tabbatuwar takararsa, amma sai daga al’amarin ya sauya.

Magoya bayan sun bayyana takaicinsu duk da cewa ana tunanin ministan ya janye takarar ne bisa bin umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daya daga cikin na kusa da mai taimaka wa ministan, Muhammad Noor, ya ba da hakuri tare da yin addu’ar fatan samun kyakkyawan sakamako fiye da takarar gwamna, haka kuma ya yi godiya ga masoyan mai girma ministan shari’a.

Haka nan shi ma wani masoyin Abubakar Malami, Musa Bello Dikko ya bayyana irin halin da Masoyan Malami ke ciki dangane da janyewar takararsa, inda ya ce, “Ni masoyin mai girma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne a nan Jihar Kebbi. Zan so na gaya wa al’ummar Nijeriya irin halin da masoya mai girma Ministan Shari’a, Abubakar Malami suke ciki dangane da janyewar takarar kujerar gwamna Jihar Kebbi a 2023.

“Hakika mun samu wannan labarin ta yadda ba mu yi zato ba, saboda duk wanda ya ji wannan labarin, to ya ji shi kwatsam babu shiri.

“Kuma mutane sun shiga jimami na ganin irin alkairi da ake sa ran ministan shari’a ya zo wa Jihar kebbi da shi, amma yanzu abin ya kubce wa jihar.

Karanta wannan  Kuma Dai: An sake maye Sabon akanta janar din da aka dora saboda EFCC na bincikensa kuna yawa gwamnati tonon silili

“Kuma mu masoyan minista muna cikin damuwa matuka da tunanin makomarmu a cikin siyasar jihar, domin abin ya kasance duk inda wani ya ga abokin tafiyarsa, to dole sai sun yi wa juna jaje, abin ya zama tamkar inda aka yi hasarar rayuka.

“Amma kuma inda muka sa kaifin basira akwai abin da Ubangiji yake nufi da yin haka. Saboda Ministan Shari’a, Abubakar Malami da uwar gidansa Hajiya Aisha Abubakar Malami, a kullum suna addu’a wajen rokon Ubangiji abin da ya fi zama alkairi, to ga hasashenmu, Allah ya amsa wannan addu’ar.

“Hakikanin gaskiya al’ummar Jihar Kebbi na bukatar kaunar Abubakar Malami ya zama gwamnan jihar. Domin idan ka duba za ka ga daga ranar da wannan sanar-wa ta fito, za ka ga mutane duk sun shiga wani yanayi na jimami da bakin cikin rashin samun ministan shari’a a matsayin gwamnan jihar.

“Saboda talakawan jihar sun ce zaben Abubakar Malami a matsayin gwamna ita ce kawai hanyar da za su iya rama masa da alkairi da ya yi musu lokacin da ba shi da bukata gare su.

“Amma daga karshe, mun shirya malamai da za mu fito fili mu yi masa adu’o’in samun nasara ga duk inda ya dosa.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.