fbpx
Friday, February 26
Shadow

Mahaifi ya hadiyi Zuciya ya Mutu bayan da ‘yan Bindiga suka sace ‘ya’yansa mata 2 a Katsina

Wani mahaifi, Hassan Bahago ya hadiyi zuciya ya mutu bayan da ‘yan Bindiga suka shiga har gidansa dake Shagari Quarters a garin Funtua suka sace ‘ya’yansa mata 2.

 

Mahaifin ya rasu ne a daidai lokacin da ‘yan Bindigar ke tafiya dashi da ‘ya’yan nasa 2, Saratu da Jennifer inda shi ya fadi kuma nan take ya mutu.

 

Yan Bindigar sun kuma sace wani Mr. Alex tare da kashe wani Alhaji Ali Bahago wanda shugaban ‘yan Bindigar yankinne.

 

Wanda ya hadiyi zuciyar ya mutu dai na daga cikin dattawam cocin ECWA ta Funtua.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *