fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Mahaifin Aubameyang ya bukaci yaran nashi da ya ci gaba da wasa a kungiyar Arsenal

Mahaifin Pierre Emerick Aubameyang wato Pierre Francois ya saka wani sabon hoto a shafin shi na Instagram wanda asalin hoton yake nuna lokacin da Arsenal suke yima yaran nashi kwantiraki a shekara ta 2018 bayan sun siye shi daga kungiyar Borussia Dortmund.

Pierre Francois yayi wani rubutu a jikin hoton yayin da yake cewa “kasan abun da zaka yi dan uwa”. Wannan rubutun da yayi yana nuna cewa yana so yaran nashi ya cigaba da wasa a arewacin landan.
Aubameyang yana kokari sosai a kungiyar yayin da yayi nasarar jefa kwallaye har guda 49 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 10 a wasanni guda 75 daya buga na premier lig.
An samu labari daga Mirror cewa kwantirakin Aubameyang zai kare ne nan da kakar wasan badi kuma har yanzu basu sasanta da dan wasan ba gami da sabon kwantiraki ba, yayin da Aubameyang yake so a kara mai albashi akan euros 200 da suke biyan shi a kowane mako.
Kungiyar Real Madrid, Barcelona, Chelsea da Manchester United suna da ra’ayin siyan dan wasan. An samu labari cewa Arsenal zasu siyar dan wasan mai shekaru 30 in har bai amince da sabon kwantiraki ba saboda basa so su rasa shi a kyauta idan kwantirakin shi ya kare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Ronaldo ya cewa Manchester ba zai halacci atisayi yau ba bayan data cigaba da ce masa ba zata sayar dashi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published.