fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Mahaifin me kudin Duniya, Bill Gates ya mutu

Mahaifin me kudin Duniya, Bill Gates watau  Bill Gates Sr. Ya mutu.

 

Ya mutu ne a Ranar Litinin kamar yanda NYT ta ruwaito.  Ya mutu yana da shekaru 94 a Duniya.

Tsohon Lauyane wanda da taimakonsa ne dan nasa, Bill Jr. Ya kafa gidauniyar tallafawa jama’a mafi girma a Duniya me suna Bill and Melinda Gates Foundation.

 

A shekarar 1994 ne Bill da mahaifinsa da matarsa sun je kallon fim a Sinima, sai yake gayawa mahaifin nasa cewa yana ta samun bukatar neman tallafi daga jama’a amma kuma bashi da lokacin kulasu saboda aiki ya masa yawa. A nan ne sai mahaifin yace shi ya bashi dama ya kula da wadannan bukattu, wanda hakanne ya kai ga kafa gidauniyar wadda a farko aka saka mata sunan William H. Gates Foundation kuma a karin farko Bill Jr. Ya saka kudi dala Miliyan 100 dan baiwa jama’a tallafi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *