fbpx
Friday, July 1
Shadow

Mahaifiyar Guardiola mai shekaru 82 ta mutu bayan kamuwa da cutar Coronavirus

Mahaifiyar Guardiola ta mutu bayan kamuwa da cutar Coronavirus

Mahaifiyar Pep Guardiola, ‘yar shekara 82, ta mutu bayan da ta kamu da cutar coronavirus, a sanarwar da kulab din Manchester City ya fitar a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da kulab din ya fitar da cewa “Ilahirin mambobin kulab din Manchester City sun yi matukar bakin ciki game da rahoton mutuwar mahaifiyar kocin kungiyar mai suna Dolors Sala Carrio wacce ta mutu a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 a Manresa dake Barcelona.

Guardiola, mai shekaru 49, a watan da ya gabata ya ba da gudummawar Euro miliyan ɗaya ($ 1 miliyan) a matsayin gudunmawarsa don yaƙi da cutar Coronavirus a ƙasarsa ta Spain.

Leave a Reply

Your email address will not be published.