fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Mahara sun rika cire idanu da wasu sassan mutane suna tafiya dasu a Kudancin Kaduna>>Cewar Wani Kansila da ya tsira

Wani Kansila a karamar hukumar Zangon Kataf dake kudancin Kaduna wanda ya tsira daga harin ranar Larabar data gabata, Cleophas Yohana, ya bayyana cewa, jami’an tsaro na baiwa maharan goyon baya.

 

Yace yana kauyen Kurmin Masara ne wanda ya kasu kashi 3 kuma an kashe mutane akalla 24 a kauyen.

Da yake bayyanawa Vanguard yanda lamarin ya faru yace an gaya musu cewa maharan na zuwa amma sai suka dauka ba da gaske bane.

 

Yace can cikin dare sai suka fara jin harbe-harbe. Yace sun je kaiwa mutanen dauki amma sai suka ji suma kauyensu an kai harin, yace koda suka dawo gida sai suka tarar an kone kusan rabin gidajen garin.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

 

Yace wasu an konesu da ‘ya’yansu a cikin gida. Ya kara da cewa akwai wanda aka kawo gawarsa an cire ido da wasu sassan jikin kuma an tafi dasu. Yace gwamnatin jihar bata yi Allah wadai da harin ko jajanta musu ba.

 

Yace kuma da jami’an tsaro suka je garin sai maharan suka rika jinjina musu, su kuma suka rakasu suka bar garin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.