Kimanin karfe biyun daren jiya juma’a barayi masu satar mutane suka kai hari garin Kunduru ta karamar hukumar kankiya a jihar katsina, inda suka ta fi da Galadiman Kundura Alhaji Ibrahim mai shekaru 91.
Alhaji Ibrahim wanda ba shi da cikakkiyar lafiya, mahaifi ne ga babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar katsina Malam kasimu Ibrahim.
Rahotanni daga garin sun tabbatar cewa maharan sun zo a Babura ne kuma suka ta fi da shi a babura.
Har ya zuwa hada wannan rahoton dai maharan ba su tuntubi iyalan Galadiman ba.