Mai kudin duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na shahararren kamfanin motar Telsa.
Musk ya sayar da wannan hannun jarin nasa ne kan maka shi a kotu da kamfanin sada zumunta ta Twitter tayi.
A baya Elon Musk ya taya kamfanin sada zumuntar ta Twitter a farashin dala biliyan 44 amma sai yasa fasa kan akwai wasu asusu na bogi da yawa a ciki.
Wanda hakan ne yasa masu kamfanin suka fusata suka maka shi a kotu, inda za a saurari shari’ar a ranar 17 ga watan Augusta.
Kuma Musk yace ya sayar da wannan hannun jarin nasa ne koda watakila idan ya fadi shari’ar sai ya saya kafar sada zumuntar.
Yayin da kuma har yanzu dai yake da hannun jari a kamfanin motar na miliyan 155.04.