Mai martaba sarkin Musulmi na kasar Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar II dake jihar Sokoto ya bukaci ‘yan uwa musulmai su fara neman jinjirin watan Dhul Hijja.
Alhaji Abubakar ya bayyana hakan ne a wata wasika data fito daga wurin shugaban majalisar musulmi a jihar Sokoto, Sambo Janaidu.
Inda yace mai martaba Sarkin Musulni yace a fara neman jinjirin watan Dhul Hijja daga ranar 29 ga watan Yuni.