fbpx
Wednesday, July 15
Shadow

Mai martaba sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris yace ranar lahadi za ai sallar Eidi a Zariya

Mai martaba Alhaji Shehu Idris ya umarci al’ummar masarautar zazzau dake jihar kaduna da a gudanar da sallah a ranar lahadi, bisa sanarwar mai alfarma sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar.

 

Hakan yazo ne bayan wasu labarai da ke yaduwa cewa masarautar ta samu rahotan ganin jinjirin watan shawwal, wanda masarutar ta bayyana cewa al’umma dadama sun kawo mata rahoton ganin jinjirin wata amma bata fitar da sanarwa ba, amma bisa sanarwar sarkin musulmi za ai sallar Eid a ranar Lahadi a cewar Masarautar.

Yanzu haka ana sa ran kara tashi da Azumi a gobe Asabar, wanda zai zama an cike Azumi 30.

 

Ya zuwa yanzu kasashan musulmai dake fadin Duniya za su gudanar da Sallah a ranar Lahadi 24 ga watan mayu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *