fbpx
Monday, August 15
Shadow

Mai sayar da burodi da ‘yan bindiga sukayi garkuwa dashi a jihar Osun ya samu yanci

Hukumar ‘yan sandan jihar Osun sun tabbatar da cewa Sikiru Ayinde mai sayar da birodi da ‘yan bindig sukayi garkuwa dashi ya samu yanci.

A ranar litinin ‘yan bindigar sukayi garkuwa dashi bayan daya je kaiwa abokan kasuwancinsa burodin su saya.

Kuma ‘yan bindigar sun bukaci kudin fansa har naira miliyan biyar kafin su sako shi, amma ‘yan uwanshi sun sasanta akan naira 150,000 kafin su sako shi jiya.

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da sakin nasa amma bata tabbatar da bayar da kudin fansar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.