fbpx
Monday, May 23
Shadow

Maimakon kara ciwo bashin Tiriliyan 6, an baiwa shugaba Buhari shawarar ya sayar da Najeriya kawai

Tsohon Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Timi Frank ya yi Allah wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na sake ciwo bashin Tiriliyan 7 dan cike gibin kasafin kudi.

 

Timi Frank yace, maimakon ciwo bashi, kamata yayi kawai shugaban kasar ya sayar da kasar dan musan cewa mun koma bayi da hujja.

 

Shugaba Buhari ya aikewa da majalisar tarayya bukatar ciwo bashin wanda yace na cike gibin kasafin kudi ne.

 

Saidak Timi Frank yace wannan sam ba abun da zai amfani ‘yan Najeriya bane dan haka bai kamata ba.

1 Comment

  • Najib musa bako

    Gaskiya kamata yayi yasayar da kasar kawai tunda burinsa wargazatane. shugaban kasa kuma ministan mai alokaci guda kuma wai arasa mapita? ina cika baki da yatayi?

Leave a Reply

Your email address will not be published.