fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Mainz sun bata ran kun Dortmund yayin da suka buga wasa jiya wanda suka tashi 2-0

Dortmund sun kasance na biyu a gasar Bundlesliga bayan jiya kungiyar Mainz sun yi nasara a kansu yayin da suka tashi wasan 2-0. Abokan hamayyar Dortmund Bayern Munich sune suka lashe kofin gasar Bundlesliga ranar talata karo na takwas a jere.

Dortmund sun yi kokari sosai a lokacin da aka fara buga wasan amma sun kasa jefa kwallo cikin ragar Mainz. Jonathan Burkardt ne ya fara cin kwallon a wasan a minti na 33 kafin aje hutun rabin lokaci, yayin da Ridle Baku ya bugo kwallon shi kuma dan wasan mai shekaru 19 yayi nasarar cin kwallon da kai.
Duk da cewa zakarun yan wasan Dortmund guda uku Jadon Sancho, Thorgan Hazard da Erling Braut Haaland suna cikin wasan kungiyar bata ci kwallo ba. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci wasan ya kara yiwa kungiyar Dortmund muni, yayin da aka ba Mainz penariti kuma Mateta yayi nasarar cin kwallon wadda tasa suka tashi 2-0.
Wannan shine karo na biyu da kungiyar Mainz taci Dortmund a kakar wasanni uku. Nasarar da Mainz suka yi tasa yanzu maki biyu suke bukata cikin wasanni biyu da zasu buga domin su tabbatar da cewa suna cikin gasar a kakar wasan 2020/21.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Duminsa: Tawagar motocin gwamna Ortom sun yi mummunan hadari

Leave a Reply

Your email address will not be published.