fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Majalisa naso a cire kayyade yawan shekaru daga sharudan daukar aiki

Majalisar Dattijai ta bukaci gwamnati da ta sa ma’aikatan Kwadago sake duba dokokin daukar aiki dan cire kayyade shekaru a wajan daukar aiki.

 

Sanata Ibrahim Gobir ne ya taso da maganar a Majalisar inda yace kayyade shekarun na hana matasa masu kwazo da hazaka wajan neman wasu ayyukan.

Yace kuma hakan na tilasta wasu matasan rage shekarunsu saboda idan ba haka ba, ba zasu yi nasara wajan samun aikin ba. Ya kara da cewa ya kamata a duba wannan lamari, lura da cewa akwai yawaitar rashin aikin yi a Najeriya kuma wani matashin sai ya kammala makaranta da shekaru 10 yana neman aiki be samu ba.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Sanata Bala Ibn Na Allah ya goyi bayan wannan kudiri.

 

Shima kakakin majalisar, Sanata Ahmad Lawal ya goyi bayan wannan kudiri inda yace sai a saka aiki ace ana neman ‘yan shekaru kawai wanda kuma wani ya kammala karatu shekaru 10 da suka gabata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.