fbpx
Monday, August 8
Shadow

Majalisa sai aukin bincike amma ba daukar mataki

Majalisar tarayya a matsayin daya daga cikin ayyukanta ta na bincike dan ganin ta gano aikata ba daidai ba a cikin ma’aikatun Gwamnati.

 

Saidai hakan yasa ‘yan Najeriya da dama na kallon wannan bincike a matsayin marar Amfani tunda dai ba’a daukar matakin da ya dace ko da an yishi.

Ba a wannan gwamnatin kadai bane majalisa ta yi bincike-binciken da ba’a dauki wani mataki akansu ba.

 

Majalisar a baya ta yi bincike akan ma’aikatun gwamnati irinsu, hukumar kula da Fansho ta kasa, PenCom wadda aka binciki batan biliyan 33.

 

Akwai biciken Hukukmar Kwastam na Tiriliyan 30 kan kudin harajin fito da aka yi wanda majalisar data gabata tace ta kwato Biliyan 140 daga ciki amma har ta sauka ba’a gabatar da wani bayani akai ba.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ba zata iya aro kudi ta biyawa ASUU bukatunta ba, tace iyaye su roki kungiyar malaman ta janye yajin aiki

 

Akwai wani aiki na bincikar dala Biliyan 16 na aikin hakar man fetur wanda shima majalisar ta bincika amma shiru. Ire-iren wadannan binciken na nan da yawa.

 

Masana dai na ganin dan amfanin kasa da ci gaban tattalin arziki ya kamata a rika daukar mataki bayan binciken majalisar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.