fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Majalisa ta Amince da kasafin kudin shekarar 2022, zata mikawa shugaba Buhari kassafin kudin a yau

A yaune ake sa ran majalisar tarayya zata mikawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kasafin kudin shekarar 2022 bayan amincewa dashi.

Tun a jiya ne dai majalisar ta amince da kasafin kamar yanda rahoton BBChausa dake kasa ya nunar.

‘Yan majalisar dattawa a Najeriya sun amince da kasafin kudin shekarar 2022 wanda shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu da ya haura sama da naira tiriliyan 16.

Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawal ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce sun yi aiki tare da bangaren zartaswa tare da cika alkawarin da suka dauka na amincewa da kasafin kafin hutun kirmisimeti.

Karanta wannan  Tuna baya: Tinubu ya taba cewa al'ummar Najeriya Obasanjo shugaban masu magudin zabe a tarihi

Ahmad Lawal ya ce akwai wadanda ke ganin ba su iya cimma wannan wa’adi ba, amma sai ga shi majalisar na kokarin nade tabarmar wannan shekarar da nasarar cika babban alkawari.

A lokacin da ya gabatarwa ‘yan majalisar kasafin kudin, shugaba Muhammadu ya ce zai mayar da hankali wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara a cikin kasafin na sama da tiriliyan 16.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.