Majalisar Dattijai ta bukaci da a saka Almajirai cikin tsarin Ilimin Boko dan maganin yanda yara Almajirai ke watangaririya a kan titunan Arewa.
Hakan ya bayyanane a zaman majalisar bisa shawarar kwamitin dake kula da ilimin bai daya na majalisar.
Shugabar Kwamitin, Sanata Akon Eyakenyi ce ta bada wannan shawara inda tace Almajiran da yawanci suke a Arewa na daga cikin mutanen da zasu amfana da tsarin dokar ilimin bai daya.
Tace gwamnatin tarayya ta samo bashin sama da Miliyan 600 dan habaka ilimin yara da basu iya zuwa makaranta wanda kuma Almajiran na cikinsu.
Majalisar ta kuma amince da kudirin kafa jami’ar Sojoji a Garin Biu, Jihar Borno, bisa kudirin da shugaban kwamitin sojojin, Sanata Ali Ndume wanda ya bayyana cewa jami’ar zata kasance me taimakawa wajan habaka harkar ilimi.