fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Majalisar dokokin Chadi ta soke hukuncin kisa kan ‘yan ta’adda

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da wata doka da ta hana aiwatar da hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da aikata laifuffukan da suka shafi ta’addanci.

 

 

Ministan shari’ar kasar Djimet Arabi ya sanar da dfaukar matakin, shekaru 4 bayan Chadi ta jingine aiwatar da hukuncin kisa kan kowanne laifi.

 

 

Arabi wanda ya gabatar wa majalisar dokoki da kudirin yace ‘yan majalisun sun amince da dokar ba tare da hamayya ba.

 

 

Ministan yace matakin wani yunkuri ne na samar da dokar bai daya kamar yadda kasashen yankin Sahel suka yi, kuma dokar zata fara aiki da zarar shugaba Idris Deby ya rattaba hannu akan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.