‘Yan majalisar dokokin jihar Katsina sun bukaci gwamnatin jihar da ta maido da hanyoyin sadarwa a sassan jihar tare da sake duba dokar kalubalantar tsaro.
An yi wannan kiran ne a lokacin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Batsari, Jabir Yusuf Yauyau, ya gabatar da kudiri mai muhimmanci na jama’a a gaban majalisar a ranar Larabar yayin zaman majalisar.
An gabatar da kudirin ne sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu 13 a karamar hukumar Batsari da ke jihar.
A cewar Yauyau, “Babban abin da ya fi damun al’amarin shi ne yadda babu wata hanyar sadarwa da al’ummar garin Batsari za su sanar da jami’an tsaro harin yayin da ake ci gaba da kai harin.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake duba matakan tsaro da ta dauka, musamman kawar da ayyukan sadarwa, yana mai jaddada cewa rashin hanyoyin sadarwa ya kara ta’azzara lamarin.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Agusta ne Gwamna Aminu Masari ya sanya hannu kan dokar kalubalantar tsaro a jihar, inda gwamnati ta dauki matakai 12 na dakile ‘yan fashi a jihar.