by hutudole
Majalisar Dokokin jihar Sakkwato ta zartar da kudirin dokar kafa Hukumar Hisba ta jihar.
Hakan ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin hadin gwiwa na majalisar kan lamuran Addini, Shari’a da ‘Yancin Dan Adam a zauren taron.
Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin Alhaji Abubakar Yabo (APC- Yabo), ya ce kwamitin ya tattauna sosai tsakanin masu ruwa da tsaki kafin ya kai ga yanke shawara.
‘Yan majalisar sun amince da rahoton ne baki daya bayan kada kuri’ar da kakakin majalisar Aminu Achida wanda ya jagoranci zaman majalisar.