fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Majalisar Malamai ta jihar Kano ta musanta zargin da ake mata na goyan bayan takarar Bola Tinubu a kakar zabe mai zuwa

Shugaban Majalisar malamai Malam Ibrahim Khalil shine ya musanta wannan zargi a yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kano.

Malamin ya ce, ko kadan babu wannan maganar hasalima ya cika da mamakin masu yada wannan batu.

A cewarsa, Majalisar Malamai bata goyan bayan wani Dan takara, inda ya kara da cewa Bola Tinubu ya zo ne jahar kano domin halartar taron bikin aure.

Idan zaku tuna Jigo a jam’iyyar APC Ahmad Bola Tinubu ya kai ziyara jihar Kano a makon da ya gabata domin halartar taron bikin aure da aka gudanar a jihar na ‘ya ga shahrararan malamin Addinin Musulunci Bin Usman lamarin da ya janyo cece kuce.

Karanta wannan  Na So A Ce Ana Kai Ziyara Lahira, Da Na Ziyarce Ki, Cewar Matashin Da Budurwar Sa Ta Rasu Ana Dab Da Aurensu

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.